Gwamnatin babban birnin tarayya na Najeriya ta bayyana cewa, zazzabin na Lassa ya tsallako cikin yankunan ta wanda a halin yanzu an tabbatar da kwayoyin cutar a jikin wasu mutane uku cikin watanni uku da suka gabata.
Dakta Humphrey Okorouku, Daraktan ma'aikacin lafiya na birnin shine ya bayyana hakan a wata ganawa da 'yan jarida na kamfanin dillancin labarai na kasa a ranar Juma'ar da ta gabata.
Rahotanni sun bayyana cewa, mutum daya cikin ukun da suka kamu da wannan cuta tuni ya riga mu gidan gaskiya a watan Janairun da ya gabata na shekarar 2018.Okoroukwu ya bayyana cewa, an tabbatar da bayyanar cutar a tantagwaryar birnin Abuja, sai dai a na sa ran waraka ta sauka nan ba da jimawa ba.
Darakta Okoroukwu ya nemi al'ummar birnin tarayya da kewayan sa kan kwantar da hankullan su, inda ya gargade su da su bayar da muhimmanci na gaske wajen tsaftace wuraren su na zama da kuma muhallai.
Babban ma'aikacin ya kuma gargadin al'ummar da su dauki dabi'un wanke hannayen su tare da watsi da ababen da ka iya janyo ma su beraye a zamantakewar su.
Jaridar NAIJ ta kuma ruwaito cewa, wani Karen Mota ya kashe Ubangidan sa murus ya kuma ya yi awon da gaba da motar sa bayan ya jefar da gawar sa a wani daji na jihar Ogun.
Source :naij hausa
Title :
Zazzabin Lassa Ya Tsallaka Birnin Tarayya
Description : Gwamnatin babban birnin tarayya na Najeriya ta bayyana cewa, zazzabin na Lassa ya tsallako cikin yankunan ta wanda a halin yanzu an tabbatar...
Rating :
5