Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa zata ci gaba da aiki a koda yaushe domin ganin ta inganta tattalin arziki da zai dauki nauyin ma’aikatan Najeriya da iyalansu.
Shugaban kasa Buhari ya bayyana cewa ya fara da duba zuwa ga albashin mafi karanci.A bisa wata sanarwa daga kakakinsa Mista Femi Adesina, shugaban kasar ya bayyana hakan a sakon taya murnar cika shekaru 40 da kafa kungiyar kwadago ta kasa.
Buhari ya bi sahun dukkan ma’aikatan Najeriya, masu ritaya day a fansho wajen murnar mataki da wannan kungiya ta kai, inda ya bayyana cewa kudi ya biya kudin sabulu na kafa wannan kungiya.
Ya ba da tabbacin cewa kungiyar kwadago ta maida hankali wajen hada kan dukkan ma’aikata ta hanyar Magana da murya daya tare da sasanta abubuwa domin ci gaban tattalin arzikin Najeriya.
Buhari ya yaba ma shugabannin kungiyar na baya da na yanzu bisa gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban kasar wanda acewarsa sun hada da gwagwarmayarsu wajen ganin an dawo da mulkin damokradiyya da kuma fada ma wadanda ke mulki gaskiya a koda yaushe.
A halin yanzu gwamnatin tarayya ta sanar da zuwa karshen watan Satumba na wannan shekarar a matsayin lokacin da za ta fara biyan sabon tsarin albashi ga ma'aikatan ta a dukkan fadin kasar nan.
Source :naij hausa
Title :
Zan Tsaya Wa Ma'aikata - Buhari
Description : Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa zata ci gaba da aiki a koda yaushe domin ganin ta inganta tattalin arziki da zai dauki nauy...
Rating :
5