Sanata Dino Melaye yayi barazanar maka Sifeta Janar na yan Sanda, Ibrahim Idris a kotu bisa tserewar da wandanda suka zargi shi (Dino Melaye) da cewa shine ya ke biyan su da kuma saya musu makamai don tayar da tarzoma.
Melaye wanda yayi magana a Majalisa yau Laraba ya karanto sashi na 43 inda ya ce Rundunar yan sandan ta kashe wandanda ake zargin ne kuma ta sake su.
Hakan ya sa Dino ya bukaci Hukumar Yan sandan ta zakullo wandanda aka ce sun gundun ko a raye ko a mace idan ba haka ba kuma zai shigar da Sifeta Idris kara a kotu bisa yiwa rayuwarsa barazana, cin zarafi da mutuncin sa, tayar masa da hankali da kuma amfani da karfin mulki ba ta hanyar da ya dace ba.
A ranar 20 ga watan Maris ne Hukumar Yan sandan Najeriya ta gabatar da wandanda ake zargin suna yiwa Dino Melaye aiki, an kama su dauke da bindigogi kirar AK 47 da kuma wasu bindigogin guda biyar.
Sai dai abin mamaki kuma a ranar Laraba sai Hukumar Yan sanda ta bayar da sanarwan cewa wandanda ake zargin su gudu daga hannun yan sanda tare da wasu mutane hudu.
Kwamishinan yan sandan Jihar Kogi, Mr. Ali Janga ya ce wanda ake zargin su biyu: Kabiru Saidu wanda akafi sani da Osama da kuma Nuhu Salisu wanda ake yiwa lakabi da smalla sun gudu ne misalin karfe 3.21 na dare daga ofishin yan sanda na Lokoja inda suke tsare.
Source :naij hausa
Title :
Zan Maka Shugaban Hukumar Yan Sanda A Kotu Saboda Sakaci Da Aiki - Dino Melaye
Description : Sanata Dino Melaye yayi barazanar maka Sifeta Janar na yan Sanda, Ibrahim Idris a kotu bisa tserewar da wandanda suka zargi shi (Dino Melaye...
Rating :
5