Shugaba Muhammadu Buhari ya fadawa shugabanin hukumomin tsaron Najeriya cewa duk za'a gudanar da bincike kan yadda aka sace yan matan Dapchi kuma duk wanda aka samu da hannu zai fuskanci hukunci.
Shugaban kasar ya yi wannan gargadin ne a ranar Juma'a ya yin da ya ke tarbar yan matan sakandiren na Dapchi ta suka ziyarce shi a fadar Aso Villa da ke Abuja.
Duk da hakan shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatin sa a shirye take tai afuwa ga duk yan ta'addan da suka ajiye makamai kuma suka mika wuya ga hukumomin tsaro.Buhari ya kara da cewa hukumomin tsaro kuma za su cigaba da bincike kuma ba za su raga wa duk wanda aka samu suna amfani da satar yaran don cin wa wata burin siyarsar su ba.
A baya, shugaban yan sandan farin kaya na DSS, Lawal Daura ya ce saura kiris kalaman mutane a kafafen sada zumunta da kuma wadanda ba su isashen ilimi kan batun ya haifar da cikas wajen ceto yan matan.
Ya kuma kara da cewa galibin yan matan sakandiren na Dapchi suna fama da matsalar fata sakamakon rashin wanka da basuyi ba na kusan wata daya.
Source :naij hausa
Title :
Zan Hukunta Duk Wadanda Sukayi Sakaci Aka Sace Yan Matan Dapchi - Buhari
Description : Shugaba Muhammadu Buhari ya fadawa shugabanin hukumomin tsaron Najeriya cewa duk za'a gudanar da bincike kan yadda aka sace yan matan Da...
Rating :
5