Mai magana da yawun bakin Mataimakin Shugaban kasa, Laolu Akande ya bayyana cewa za a samawa jama'a aiki a Neja-Delta. Akande ya bayyana wannan ne bayan wani taro da aka yi a Ranar Juma’a tsakanin Ministocin kasar a fadar Shugaban kasa.
Mista Laoulu Akande yace za a kafa wuraren neman aiki wadanda za su yi sanadiyyar samawa Matasa 208, 000 sana’a a Yankin na Neje-Delta. Hukumar NDDC za ta taimaka wajen cin ma wannan buri na rage yawan masu zaman banza.
Bayan nan kuma akwai kananan matatu na fetur da za a kafa a irin su Jihar Ribas kwanan nan wanda za su taimakawa matasa wajen samun sana’a.
Farfesa Yemi Osinbajo yace wannan zai rage zaman kashe wando a wadannan wuraren.Haka kuma Laolu Akande ya bayyana cewa Jami’ar koyon harkar ruwa da ke Garin Okerenkoko a Jihar Delta za ta soma aiki a shekarar nan. A watan gobe ne ma ake sa rai cewa za a fara darasi a Makarantar.
Source :naij hausa
Title :
Zamu Rage Zaman Kashe Wando A Kasar Nan-Gwamnatin Buhari
Description : Mai magana da yawun bakin Mataimakin Shugaban kasa, Laolu Akande ya bayyana cewa za a samawa jama'a aiki a Neja-Delta. Akande ya bayyana...
Rating :
5