Wasu Matasa har kungiyoyi 55 karkashin tafiyar ‘Not Too Young to Run’ na masu fafatukar ganin Matasa sun samu mulkin Najeriya za su shiga Fadar Shugaban kasa a yau dinnan.
Jaridar Daily Trust ta rahoto wannan inda tace daya daga Shugabannin kungiyar YIAGA ta Matasan kasar watau Samson Itodo ya bayyana wannan a farkon makon. Matasan za su kutsa har cikin fadar Shugaban kasar na Aso Villa a yau Talatan nan.
Matasan su na nema ne Shugaban kasar ya sa hannu kan kudirin da zai ba ‘yan shekara kasa da 40 tsayawa takarar kujerar Shugaban kasa. Yanzu dai Majalisa ta rage shekarun da ake bukata na tsayawa takara inda har ‘dan shekaru 25 zai iya zuwa Majalisa.
Wadannan Kungiyoyi dai za su nemi su gana da Shugaban kasar ba tare da wani zanga-zanga ba domin ganin Gwamnatin Tarayya tayi abin da zai taimaki Matasa wanda su ne mafi akasarin ‘Yan kasar.
Source :naij hausa
Title :
Zamu Kutsa Har Fadan Shugaban Kasa Don Mugana Dashi - Kungiyar Matasa
Description : Wasu Matasa har kungiyoyi 55 karkashin tafiyar ‘Not Too Young to Run’ na masu fafatukar ganin Matasa sun samu mulkin Najeriya za su shiga Fa...
Rating :
5