Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, ya lashi takobin cewa zai dukufa wajen ganin an ceto yarinya daya tilo da ta rage daga cikin yammatan makarantar Dapchi 110 da aka sace, kamar yadda ya yi a lokacin da suke hannun 'yan Boko Haram.
A cikin wata sanarwa da mataimakin shugaban na musamman a kan harkokin watsa labarai Malam Garba Shehu ya fitar, ta ce, gwamnatin shugaba Buhari, ba za ta yi kasa a gwiwa ba a kokarin ganin ta ceto tare da dawo da Leah Sharibu, gida wajen iyayenta lami lafiya, kamar yadda aka ceto sauran yammatan, bayan da 'yan ta'addar suka rike ta kamar yadda aka rawaito cewa saboda ta ki yar da ta musulunta ne.
Sanarwar ta ce, shugaba Buhari, na cike da sanin nauyin da ya rataya a wuyansa, kamar yadda tsarin mulkin kasar ya tanadi ya kare dukkannin 'yan Najeriya, ba tare da la'akari da bambancin addininsu ko kabilarsu ko kuma yankin da suka fito ba, kuma ba zai gajiya ba wajen sauke wannan nauyi.
Kazalika sanarwar ta ce, shugaban na sane da fadar cewa, dukkannin musulmai na gaskiya a fadin duniya, suna martaba ka'idar nan da ke cewa babu tilas a addini.
A dangane da haka, babu wani mutum ko wata kungiya da za ta tilasta addininta a kan wani.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, shugaban na Najeriya, na cike da alhini ga iyayen wannan yarinya, wadanda za su rinka kallon sauran takwarorinsu da aka sako 'ya'yansu na murna, yayin da su kuma 'yarsu har yanzu ba ta tare da su.
Daga karshe sanarwar ta ce, shugaba Buhari, ya jaddada cewa ba za a yi watsi da wannan yarinya da ta rage ba, kuma nan bada jimawa ba, iyayenta za su kasance cikin murna tare da 'yarsu.
A watan jiya ne dai aka sace yammatan, lamarin da ya janyo mummunar suka kan gwamnati da jami'an tsaron Najeriya.
A ranar Jumma'a ne ake kyautata zaton shugaba Buharin, zai karbi yammatan na Dapchi a fadarsa da ke Abuja.
Source :bbc hausa
Title :
Zamu Kubutar Da Daliban Dapchi Data Rage - Buhari
Description : Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, ya lashi takobin cewa zai dukufa wajen ganin an ceto yarinya daya tilo da ta rage daga cikin yammatan ...
Rating :
5