Shugaba Muhammadu Buhari a jiya, a ofishinsa, a birnin tarayya, ya karbi ‘yan matan makarantar Dapchi da aka saki kuma ya bayyana cewa zai karbi tubar 'yan kungiyar Boko Haram da suka ajiye makamai kuma suka mika wuya.
Shugaban kasar ya kara da cewa gwamnatinsa a shirye take da ta bawa wadanda suka mika wuya kula ta musamman don ci gaba da rayuwa a cikin wannan al’umma tamu mai girma.Yace, “gwamnati na iyaka gwargwadon kokarinta don ganin cewa an saki kowane dan kasa dake hannun ‘yan ta’adda”.Shugaban kasar ya gargadi shuwagabannin tsaro akan cewa idan aka samu wata baraka ko yaya ta ke daga bangarensu, za'a hukunta su.
Yace, ya rataya wa dukan jami’an tsaro nauyin kiyaye kara aukuwar satar ‘yan makaranta a duk fadin kasar nan.A kokarin da gwamnatinsa ke yi na yaki da ta’addanci, Buhari bukaci dukan ‘yan Najeriya da su taimaka wurin gudanar da wannan aiki.
Shugaban kasar yace, kasar ta wahala sosai, don haka yana so kowa ya rungumi zaman lafiya saboda cigaban kasar.
A lokacin da ta ke jawabi a mamadin ‘yan uwanta, Fatima Bashir mai shekaru 14, ‘yar aji uku, tayi godiya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, da ya ceto rayuwarsu daga hannun ‘yan ta’adda, ya kuma dawo dasu gidajen su lafiya
Source :naij hausa
Title :
Zamu Karbin Tuban Duk Dan Boko Haram Din Daya Mika Wuya - Buhari
Description : Shugaba Muhammadu Buhari a jiya, a ofishinsa, a birnin tarayya, ya karbi ‘yan matan makarantar Dapchi da aka saki kuma ya bayyana cewa zai k...
Rating :
5