Yau din nan da rana aka gudanar da wani babban taron masu ruwa da tsaki na majalisar tattalin arzikin kasar nan a babban dakin taro na fadar shugaban kasar Najeriya dake a garin Abuja a karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo.
Taron wanda ya samu halartar manya masu rike da mukaman da suka danganci tattalin arzikin kasar, ya kuma samu halartar fitattun masu kudin duniyar nan watau Bill Gates da kuma Aliko Dangote.
Jaridar naij ta samu cewa a wajen taron kuma mataimakin shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo ya ayyana cewa gwamnatin su na shirin daukar sabbin ma'aikata a karkashin shirin gwamnatin na N-power har 300,000.
Source :naij hausa
Title :
Zamu Dauki Ma'aikata Da Dama A Kasarnan Wannan Shekaran - Osinbajo
Description : Yau din nan da rana aka gudanar da wani babban taron masu ruwa da tsaki na majalisar tattalin arzikin kasar nan a babban dakin taro na fadar...
Rating :
5