Shugaban Amurka, Donald Trump ya amince ya gana da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-Un.
Fadar White House ta tabbatar Shugabannin biyu za su tattauna nan gaba.
Wani jakadan Koriya ta Kudu Chun Eiu-Yong wanda ya hadu da shugabnnin biyu a cikin wannnan makon ya ce Mr Kim ya yadda zai daina duk wasu gwaje gwajen Nukiliya.
Ya kuma ce za a yi tattaunawar ne a watan Mayu.
A wani bayani da ya wallafa a shafinsa na twitter, Shugaba Trump ya ce sakon da ya samu daga Kim Jong-un ya kunshi batun dakatar da aiki da makaman nukiliya.
Sai dai Mr Trump ya ce duk wasu takunkumai za su ci gaba da tasiri har sai sun cimma matsaya.
Babu Shugaba mai ci na Amurka da ya taba ganawa da wani Shugaban Koriya ta Arewa.
Source :bbc hausa
Title :
Za'a Gana Tsakanin Trump Da Kim Jong Un A Karo Na Farko
Description : Shugaban Amurka, Donald Trump ya amince ya gana da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-Un. Fadar White House ta tabbatar Shugabannin biyu za ...
Rating :
5