Mahukunta a babbar asibitin koyarwa ta jami'ar Najeriya dake a garin Enugu, babban birnin jihar Enugu dake a yankin kudu maso gabashin Najeriya sun bayyana cewa asibitin za ta fara yin tiyatar dashin koda ga marasa lafiya masu bukata.
Wannan dai, kamar yadda muka samu yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da asibitin ta fitar dauke da sa hannun kwararrun likitoci shidda a cikin satin da ya gabata.
Jaridar naij ta samu kuma cewa hukumar asibitin ta zabtare kudin yin tiyatar daga kusan Naira miliyan 11 ya zuwa Naira miliyan 3 da rabi wanda a cewar su sun yi hakan ne domin samar da sauki ga masu bukarar hakan.
Haka ma dai hukumar gudanarwar asibitin ta zayyana cewa za su soma yin tiyatar ne a ranar 7 zuwa 14 ga watan Yulin da ke tafe don haka dukkan mai bukata sai ya garzaya asibitin domin karin bayani.
Title :
Za'a Fara Tiyatar Dashen Koda A Asibitin Koyarwa Na Enugu
Description : Mahukunta a babbar asibitin koyarwa ta jami'ar Najeriya dake a garin Enugu, babban birnin jihar Enugu dake a yankin kudu maso gabashin N...
Rating :
5