Gwamnatin tarayya na duba yiwuwar fara koyar da yara a makarantun firamare da yaren iyayensu. Za a ke amfani da yaren uwa wajen koyar da yaran da basu wuce aji uku a firamare ba.
Ministan ilimi Adamu Adamu ya bayyana haka jiya a Abuja yayin halartar wani taron rahoto a kan cigaban ilimi da bankin duniya ta dauki nauyi.
Ministan na yin wadannan kalamai ne a matsayin martani ga tambayar da aka yi masa a kan koyar da yara cikin harshen iyayen su domin saukaka koyo da koyarwa.
Darekta a bankin duniya Rachid Bennessaoud ya bayyana cewar harkar koyo da koyarwa ta wuce maganar inganta ajuzuwan daukan darasi tare da yin alkawarin hada karfi da gwamnatin tarayya domin inganta harkar ilimi.
Wasu masu nazarin harkar ilimi a kasar nan na ganin cewar tabarbarewar ilimi na da alaka da koyar da yara da yaren da ba na su ba kuma ba su da fahimtar sa a matakin koyo na farko.
Source :naij hausa
Title :
Za'a Fara Amfani Da Yaren Uwa Don Koyarwa A Makarantun Firamare
Description : Gwamnatin tarayya na duba yiwuwar fara koyar da yara a makarantun firamare da yaren iyayensu. Za a ke amfani da yaren uwa wajen koyar da yar...
Rating :
5