Wata yarinya 'yar shekaru 11 da haihuwa 'yar asalin kasar Falasdin ta shararawa wani sojan Isra'ila mari, inda hakan yayi mutukar girgiza kasar Isra'ila, inda a yanzu haka kasar ta bayyana yarinyar a matsayin barazana babba a gareta.
A rahoton da wata tashar yada labarai ta Isra'ila ta fitar, ta bayyana cewa an kulle yarinyar mai suna Janna, wacce ake ganin ta lashe lambar yabo ta zama maras tsoro.
Hukumar harkokin wajen kasar Isra'ila ta bayyana Janna, wacce ta fito daga kauyen Nabi Salih a yankin yammacin gabar kogin Jordan, a matsayin baraza mai karfi ga kasar Isra'ila.
A kwanakin baya yarinyar ta dauki hotuna da bidiyo na yadda sojojin kasar Isra'ila suke cin zarafi tare da azabtar da Falasdinawa, inda ta yada a kafafen sadarwa da shafukan Intanet.
Miliyoyin mutane na sassa daban-daban na duniya sun kalli wadannan hotunan da bidiyo wanda Janna ta saka, inda mutane suka dinga Allah wadai da irin abinda kasar ta Isra'ila ta ke yi.
Hakan da yarinyar ta yi yayi matukar razana kasar Isra'ila inda ta bayyana yarinyar a matsayin "Babbar Barazana gareta".A wata hira da aka yi da ita da kafar sadarwa ta Anadolu Agency, Janna ta ce babban burinta shine ta zama "Muryar Yaran Falasdinu".
A rahoton da kafar sadarwa ta Isra'ila ta fitar, ta ce kotu ta yanke wa Janna wacce a yanzu haka al'ummar duniya ke mata kallon "Jarumar Falasdinu", hukuncin wata 8 a kurkuku.
Source :naij hausa
Title :
Yarinyar Dake Neman Zama Barazana Da Isra'ila
Description : Wata yarinya 'yar shekaru 11 da haihuwa 'yar asalin kasar Falasdin ta shararawa wani sojan Isra'ila mari, inda hakan yayi mutuka...
Rating :
5