NneNne Iwuji-Eme, ‘yar Najeriya ce, amma mazauniyar Ingila, ta zama bakar mace ta farko da kasar Ingila ta bawa matsayin kwamishina, wadda yanzu zata wakilci kasar a Mozambique.
Jaridar UK Guardian ta ruwaito cewa NneNne Iwuji-Eme, kafin a bata wannan matsayi tayi aiki a Ofishin kasar waje na Ingila na tsawon shekaru 16, kuma zata maye gurbin Joanna Kuenssberg a watan Yuli, a matsayin babbar kwamishina.A cikin rahoto, Iwuji-Eme tana ganin matsayin da aka bata na nuna “girmamawa da karramawa.” Ta kara da cewa “ Ina fatan bani wannan matsayi a Ingila kuma bakar mace ta farko da aka bawa zai karawa matasa masu basira kwarin gwiwa ba tare da la’akari da kalar fata ko inda suka fito ba, sannan su dage wurin cimma burinsu na samun matsayi a kasar waje.
Ina shirin kara dankon zumunci tsakanin Ingila da Mozambique, wadanda dama sunada dangantaka ta bangare tattalin arzikin kasa.Sakataren waje, Boris Johnson, lokacin da yake jawabi akan matsayin da aka bawa Iwuji-Eme, yace ta hangen nesa, kuma tanada masaniya akan aikin da kuma jarumtar da zata tafiyar da aikin.
A matsayinmu na nahiya guda tareda kasashen dake tasowa ta bangaren arzikin kasa, Afirika tanada mahimmanci na hadin gwiwa.
An rawaito cewa Iwuji-Eme tayi aiki a matsayi mai kula da tattalin arziki a fannin filaye, abinci da al’amuran karkara da kuma harkar sarauta. Kafin a bata wannan matsayi, an turata kasar Brazil a matsayin Sakatare domin bada shawarwari.
Source :naij hausa
Title :
Yar Nijeriyan Da Ta Zama Kwamishina A Ingila
Description : NneNne Iwuji-Eme, ‘yar Najeriya ce, amma mazauniyar Ingila, ta zama bakar mace ta farko da kasar Ingila ta bawa matsayin kwamishina, wadda y...
Rating :
5