Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Fatai Owoseni, shine ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai a birnin Makurdi, inda yace barayin 10 sun shiga hannu sakamakon rahotannin wasu makiyaya na garin Guma da sace-sacen shanu yake ci musu tuwo a kwarya.
Owoseni ya bayyana cewa, hukumar ta 'yan sanda za ta ci gaba hada gwiwa da sauran hukumomin tsaro domin kawo karshen ta'addanci a yankunan jihar.
Kwamishinan ya kara da cewa, a halin yanzu hukumar ta cafke miyagu 44 a sassa daban-daban da suke yiwa dokar hana kiwo karan tsaye a jihar.
Tun dai an gurfanar da wannan 'yan ta'adda a gaban kuliya domin zartar musu da hukuncin da ya dace da su kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Jaridar Naij ta kuma ruwaito cewa, a ranar Talatar da gabata ne hukumar Sojin kasa ta kaddamar da wani sabon barikin soji a jihar Bayelsa.
Source :naij hausa
Title :
Yan Sanda Sunkama Barayin Shanu Goma A Jihar Benuwe
Description : Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Fatai Owoseni, shine ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai a birnin Makurdi, inda yace bara...
Rating :
5