Tsohon ministan tsaro na kasa, Janar Theophilus Danjuma (murabus) ya yi kira ga yan Najeriya su tashi su kare kansu daga masu kawo musu hari a garuruwan su.
Danjuma ya fadi wannan magana ne a yau Asabar yayin da ya hallarci taron yaye daliban jami'an jihar Taraba karo na farko kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito."Ni ba dan siyasa bane kuma ba zan iya shiga siyasa ba don idan da ace ni dan siyasa ne ba zan iya fada muku abin da na fada yanzu ba.
"Bayan na iso wajen taron nan, na ga kyawawan al'adun al'ummar mu kuma sun kyatar da ni sosai. Taraba kamar karamar Najeriya ya ke don akwai kabilu da dama a jihar kuma suna zaune lafiya amma a halin ana zaman dar-dar ne a jihar.
"Akwai masu yunkurin ganin sun kawar da wasu kabilu a jihar nan da kuma wasu kauyuka a Najeriya."Ba za mu amince ba. Dole mu taka musu birki. Kowannen mu sai ya mike tsaye." inji Danjuma
A wata labarin, jaridar naij ta kawo muku rahoton yadda hukumar binciken sirri na DSS ta yi sulhu da yan Boko Haram kafin dawo da yan matan Dapchi, A yayin da yake magana a kan irin yarjejeniyar, Lawal Daura ya ce ka'idar kawai da suka amince da ita shine tsagaita wutar wucin gadi don bawa yan ta'addan dama su dawo da yan matan inda suka dauke su.
Daura ya kara da cewa sulhun anyi shi ba wai don ceto 'yan matan Dapchi ne kadai ba amma ana son a kawo karshen hare-haren da yan ta'addan ke kaiwa wasu sassan yankunan ne.
Source :naij hausa
Title :
Yan Nijeriya Su Kare Kansu Daga Masu Kashesu - TY Danjuma
Description : Tsohon ministan tsaro na kasa, Janar Theophilus Danjuma (murabus) ya yi kira ga yan Najeriya su tashi su kare kansu daga masu kawo musu hari...
Rating :
5