Majalisar dattijan Najeriya a jiya ta tabbatar da ikirarin da Sanata Shehu Sani yayi wanda ke wakilatar mazabar shiyyar Kaduna ta tsakiya daga jam'iyyar APC na cewa kowane Sanata na karbar Naira 13.5 miliyan a matsayin kudin gudanarwa duk wata.
Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da mai magana da yawun 'yan majalisar Sanata Aliyu Sabi Abdullahi daga jihar Neja ya fitar inda ya ke tabbatar da batun sannan ya kuma ce shi Sanata Shehu Sani din bai fadi wani sabon abu ba.
Jaridar naij ta samu haka zalika cewa Sanata Sabi ya kuma karyata cewa wai 'yan majalisun sun ji haushin Sanata Sani din don ya fadi hakan a wata firar da yayi da manema labarai.
A wani labarin kuma, Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta gwamnatin tarayyar Najeriya watau Independent National Electoral Commission, INEC a takaice ta sanar da wasu muhimman sauye-sauye a kan yadda za ta gabatar da zaben shekarar 2019 mai zuwa.
Mun samu cewa hukumar ta zaben ta Independent National Electoral Commission, INEC ta ta bakin kwamishinan ta na jihar Imo Farfesa Francis Ezeonu ya bayyana cewa ba za su yi anfani da fom din nan ba na rubuta kura-kuran da aka samu watau Incident Form.
Source :naij hausa
Title :
Yan Majalisan Dattijai Sun Baiyana Kudin Dasuke Karba Duk Wata
Description : Majalisar dattijan Najeriya a jiya ta tabbatar da ikirarin da Sanata Shehu Sani yayi wanda ke wakilatar mazabar shiyyar Kaduna ta tsakiya da...
Rating :
5