Fitacciyar jarumar nan kuma tsohuwar fuska ta fina-finan Hausa a masana'antar shirya fina-finai da ake yiwa lakani da Kannywood watau Mansura Isa ta bayyana yadda aka so lalata mata aure tun tana amarya kimanin shekaru 15 da suka gabata.
Tsohuwar jarumar da ke zaman mata ga wani fitaccen jarumin kuma daya daga cikin ginshikai a masana'antar shirya fina-finan na Hausa da ma na turanci watau Sani Danja ta bayyana hakan ne yayin da ta yi wata fira da majiyar mu a kwanan baya.
A cewar ta, ita ta godewa Allah da ya sa mijin ta yana da kyakkyawar fahimta ta rayuwa sannan kuma a koda yaushe yakan bata shawarwari tare kuma da kwarin gwuiwa akan dukkan lamurran da ta sa a gaba musamman ma dai na gidauniyar ta.Haka zalika ta kara da cewa: "A farkon aurenmu mutane sun yi kiraye kiraye da turo masa tes, cewa wai, ba zama zan yi ba.
Amma cikin ikon Allah, yau da gobe ta karyata su.
Hajiya Mansura ta ce yau ga shi bayan shan gwagwarmaya kala-kala da kuma kaikomo iri-iri na aurnen na su, yau gashi har yanzu suna tare sannan kuma kauna a tsakanin su sai ma dai abun da yayi gaba.
Source :naij hausa
Title :
Yan Gulma Sunso Su Lalata Auren Mu Tun Ina Amarya - Mansura Isa
Description : Fitacciyar jarumar nan kuma tsohuwar fuska ta fina-finan Hausa a masana'antar shirya fina-finai da ake yiwa lakani da Kannywood watau Ma...
Rating :
5