Kasa da sa'o'i ashirin da hudu bayan kaddamar da taswirar shekara biyar na tsarin tabbatar da zaman lafiya a jihar Filato da shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar, ‘yan bindiga sun kashe mutune biyar.Harin ya faru ne a garin Nzharuvo na karamar hukumar Bassa ta jihar a daren ranar Alhamis.
An kai harin ne a wani gari da ke kusa da makarantar sakandare ta ECWA, Mingo, a karamar hukumar Bassa.Shugaban matasa na garin, Danjuma Auta ne ya shaidawa Jaridar Premium Times cewa, yawanci wadanda abun ya shafa yara ne sai wata mace guda daya.
Ci gaba da hare-haren da ake kawo ma al’ummominmu, yasa yawancin maza basa barci a gida. Muna cigaba da kula da iyakokinmu a yankunanmu, muna mamakin daga inda masu kawo mana hari suke zuwa.
"Wannan mummunan lamari ne, wadannan masu kisan basu da imani.
Basu da tausayi ga yara kanana da basu da laifi. Sun sassara yaran har saida suka mutu, a halin yanzu ma da muke magana muna shirin binne su ne," inji shi.Mai magana da yawun hukumar Yan Sanda na Filato Terna Tyopev, a firar da akayi dashi ta wayar salula yace bai samu labarin harin na Nzharuvo ba.
Harin dai ya faru ne duk da jawabin da hukumar Yan Sandan tayi na baza jami’ai sama da 2,000 a Filato saboda zuwan shugaban kasa.
A ziyarar sa ta kwana biyu shubagan ya kaddamar da aikin hanya wanda akasa wa sunansa.
Source :naij hausa
Title :
Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Biyar A Filato Duk Da Kasan Cewar Buhari A Garin
Description : Kasa da sa'o'i ashirin da hudu bayan kaddamar da taswirar shekara biyar na tsarin tabbatar da zaman lafiya a jihar Filato da shugaba...
Rating :
5