Faifan bidiyo ya fita inda yake dauke da shahararren hamshakin mai kudin nan na farko a nahiyar Afrika Alhaji Aliko Dangote yana ta tikar rawa a wajen walimar bikin diyar sa Fatima Dangote da ta gudana a jiya, garin Legas.
Mun samu dai cewa shahararren mai kudin dai ya taka rawar ne yayin da fitaccen mawakin nan dan asalin Najeriya Mai suna Davido ke cashewa da wakar sa mai suna 'Fia'.
Mai karatu dai zai iya tuna cewa a ranar Juma'ar da ta gabata ne dai aka gudanar da walimar kayataccen bikin nan na fada aji na diyar hamshakin mai kudin nan na nahiyar Afrika watau Fatima Dangote da kuma angon ta Jamilu Abubakar a birnin Ikko na jihar Legas.Walimar dai ta tara dukkan manyan kasar nan har ma da na kasashen waje kama da ga 'yan kasuwa, yan siyasa zuwa ga manyan jami'an gwamnati akowane mataki na kasar.
Wasu daga cikin wadanda suka halarci bikin dai sun hada da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, tare da matar sa Dolapo Osibajo, sai kuma hamshakin mai kudin nan Bill Gates da kuma matar sa Melinda Gates.
Sauran sun hada da uwar gidan shugaban kasa Aisha Buhari, Sarkin Kano Sanusi Lamido, gwamnoni da Sanatoci da 'yan majalisar wakillai da dai sauran su.
Source :naij hausa
Title :
Yadda Dangote Ya Sha Rawa A Gun Waliman Bikin Diyarsa
Description : Faifan bidiyo ya fita inda yake dauke da shahararren hamshakin mai kudin nan na farko a nahiyar Afrika Alhaji Aliko Dangote yana ta tikar ra...
Rating :
5