Almajirai yara ne a arewacin Najeriya wanda talauci yake tilasta iyayensu bada su ga wasu malaman addini domin karatu. Almajirai suna yawo lungu-lungu, gida gida da wuraren sai da abinci domin su samu wanda zai basu guntun wanda aka ci aka rage, wasu ma har shara suke bi domin su samu abinda zasu saka a bakin salatin su.
Wata sabuwar kungiya a cikin garin Kaduna mai suna Brighter Brains Institute, ta fito da wata sabuwar hanya da zata sharewa almajiran hawaye, inda zata ke raba musu abinci kamar irinsu shinkafa, nama, da dai sauransu.
Kwanakin baya ma kungiyar ta yi kokarin tallafawa kusan a kalla yara 50 da abinci, inda sanadiyyar haka yasa da yawa daga cikin almajiran basu fita yawon baran da suka saba ba a cikin garin Kadunan.
Source :naij hausa
Title :
Wata Sabuwar Kungiya Ta Fito A Kaduna Don Tallafawa Almajirai
Description : Almajirai yara ne a arewacin Najeriya wanda talauci yake tilasta iyayensu bada su ga wasu malaman addini domin karatu. Almajirai suna yawo l...
Rating :
5