Da sanadin shafin yanar gizo na lifeinsaudiarabia.net,jaridar naij ta kawo muku wasu sirrika goma da ruwan Zam-Zam ya kunsa da kuma ya dace a ce kowane musulmi ya ribaci ilimin da suke tafe da shi domin yada shi ga sauran al'umma.
1. Asalin Ruwan Zam-Zam: Dan Hajara Annabi Isma'il, tsira da aminci su kara tabbata a gare su, ya tsunduma cikin yunwa da kishirwa bayan guzuri ya yanke da mahaifin sa Annabi Ibrahim ya bari.A sakamakon tausayi da jin kai irin na uwa ga dan ta, ta shiga kai komo tare da hawa da sauka a kan duwatsun Safa da Marwa wajen neman abin da dan ta zai sanya a baka. Bayan wannan kai komo har sau bakwai sai kawai cikin mamaki ta ankare da wani ruwa dake gudana a karkashin inda sawayen dan ta, Annabi Isma'il.
2. Wasu sunaye da ake yiwa ruwan lakabi: Akan kirayi ruwan Zam-Zam da Maimoona, Shabbaa'a da kuma Murwiya.
3. Karfin jiki: Binciken wani masanin kimiyya na kasar Jamus, Dakta Knut Pfeiffer ya bayyana cewa, kwayoyin halittu na jikin dan Adam su kan zabura da zarar an kwankwadi ruwan Zam-Zam.
4. Amfani: Alfanun ruwan Zam-Zam ba su da iyaka, ya kan biya bukata duk wata niyya da aka sha ruwan domin ta.
5. Kiwon Lafiya: Ruwan Zam-Zam ya kunshi sunadaran Magnesium da Calcium dake kawar da wata cuta mai kwazaba.
6. Tarihi: Tun shekaru sama da 4000 da suka gabata, ruwan Zam-Zam yake ta gudana ba bu kakkautawa.
7. Tsafta: Bincike ya bayyana cewa ba bu wani tsaftaceccen ruwa da zai goga kafada da ruwan Zam-Zam.
Source :naij hausa
Title :
Wasu Sirrika 7 Dake Kunshe A Cikin Zam Zam
Description : Da sanadin shafin yanar gizo na lifeinsaudiarabia.net,jaridar naij ta kawo muku wasu sirrika goma da ruwan Zam-Zam ya kunsa da kuma ya dace ...
Rating :
5