Mutane uku ne aka tabbatar da sun rasa ransu yayin da wasu 'yan bindiga su ka kai hari kauyen Tandama dake karamar hukumar Danja a jihar Katsina.
Wani shaidar gani da ido da aka kashe dan uwansa ya ce 'yan bindigar, cikin kakin soji, sun dira a kauyen da misalin karfe 1:15 na safiyar ranar Asabar dauke da bindigu kirar AK 47. 'Yan bindigar sun kai farmaki gidajen Alhaji Safiyanu da Abdullahi Tandama.
Saidai, tirjewar da mutanen kauyen su ka yi tare da tunkarar 'yan bindigar ya yi sanadiyar mutuwar biyu daga cikin 'yan fashin yayin da su ka kashe mutum daya daga mutanen garin.
"Dan uwana na kawance a waje sai su ka ji karar harbin kuma su ka tashi tare da tunkarar 'yan fashi domin hana su aikata abinda su ke da niyya.
Saboda mutanen garin na da yawa, sun yi nasarar fin karfin 'yan bindigar tare da hallaka biyu daga cikinsu yayin da su kuma su ka kashe dan uwana sannan su ka gudu bayan jin isowar 'yan sanda.
"Saidai hukumar 'yan sanda a jihar Katsina ta bayyana cewar 'yan bindigar biyu sun mutu ne yayin musayar wuta da jami'an ta.
Kazalika hukumar ta sanar da baza jami'anta masu yaki da fashi da makami domin cafko ragowar 'yan bindigar da su ka gudu.
Source :naij hausa
Title :
Wasu 'Yan Bindiga Cikin Kakin Sojoji Sun Kai Hari Katsina
Description : Mutane uku ne aka tabbatar da sun rasa ransu yayin da wasu 'yan bindiga su ka kai hari kauyen Tandama dake karamar hukumar Danja a jihar...
Rating :
5