Wani rahoto da jaridar naij ta ci karo da shi ya bayyana cewar wani mutum ya dauki doka a hannunsa ta hanyar datse kafar wani gardi mai shekaru 36 da ya yiwa diyarsa 'yar watanni 6 fyade a jihar Edo.
Jaridar Naij ta ci karo da wannan labari ne ta shafin wani mutum, Prince Gwamnishu Harrison, a dandalin sada zumunta. Ya bayyana cewar, mahaifin jaririyar, ya kama mutumin na saka yatsa a al'aurar diyar sa. Amma sabanin sanar da hukuma sai kawai ya dauki doka a hannunsa.
Harrison ya kara da cewa, mahaifin jaririyar bai wani bata lokaci ba wajen dauko adda tare da kaftawa mutumin sara a kafa bayan ganin abinda yake aikatawa.
Yanzu haka dai an garzaya da mutumin asibiti yayin da shi kuma uban yarinyar ake tsare da shi a ofishin hukumar 'yan sanda bisa laifin daukan doka a hannunsa.Ko a satin da ya gabata saida naij ta kawo maku labarin wani magidanci, Ajidare Oluwadare, mai shekaru 52 a duniya ya gurfana gaban kotun majistare dake Ikorodu a jihar Legas bayan samun an same shi da laifin wasa da nonon kwaila.
Dan sanda mai gabatar da kara, Saja John Iberedem, ya shaidawa kotun cewar wanda ake tuhumar ya aikata laifin ranar 26 ga watan Fabrairu da misalin karfe 4:00 na yamma.
Source :naij hausa
Title :
Wani Uba Ya Datse Kafar Wanda Yayi Wa Yarsa Fyade
Description : Wani rahoto da jaridar naij ta ci karo da shi ya bayyana cewar wani mutum ya dauki doka a hannunsa ta hanyar datse kafar wani gardi mai she...
Rating :
5