Mun samu labari cewa Sanatan Arewacin Jihar Borno Abubakar Kyari ya dauki nauyn karatun ‘Dalibai 500 da ke Makarantun da ke gaba da sakandare daga Mazabar sa. Yanzu haka ma Sanatan zai kara taimakawa wasu.
Daga cikin wadanda aka taimakawa, akwai ‘Dalibai 100 daga Jami’ar Maiduguri sai kuma wasu ‘Dalibai 400 da ke karatu a Makarantun da ke cikin Jihar Borno
. Honarabul BG Galangi ya bayyana wannan a wancan makon na jiya.
Honarabul Babagana Galangi wanda shi ya wakilci Sanatan a taron ya bayyana cewa burin Sanata Kyari shi ne ya ga Jama’a sun yi karatun Boko. Galangi ya zayyano wasu kadan daga cikin manyan ayyukan Sanatan a wurin taron.
Source :naij hausa
Title :
Wani Sanata Zai Taimaka Wa Dalibai 1000 A Yankinsa
Description : Mun samu labari cewa Sanatan Arewacin Jihar Borno Abubakar Kyari ya dauki nauyn karatun ‘Dalibai 500 da ke Makarantun da ke gaba da sakandar...
Rating :
5