Kai jama’a, wai menene bukatar mutanen zamanin nan ne? Arziki, aure, yaya, ilimi, suna, ko me? Saboda a gaskiya yadda mutane ke kauce hanya domin son zuciyarsu, a iya cewa ko a zamanin jahiliyya sai haka. Shafin Rariya dake kafar sadarwar zamani na Facebook ta kawo mana rahoton wani matashi mai tsananin son duniya da aka kama shi cikin wani mummunan hali a wani Masallaci dake jihar Zamfara.
Wannan abu mara dadin ji ya faru ne a garin Mada na jihar Zamfara, inda aka cafke wannan matashi da ba’a bayyana sunansa ba yana kwance tsirara a cikin Masallaci, sa’annan ya yi matashin kai da Al-Qur’ani mai tsarki, kamar yadda majiyar NAIJ.com ta ruwaito. Matashin Majiyar ta kara da cewa matasan garin Mada sun kama wannan matashi cikin wannan hali ne a daren talata, 27 ga watan Feburairu,wayewar garin Laraba. Jama’an da suka kama shi, sun bayyana cewa mutumin dan asalin garin Gusau ne, babban birnin jihar Zamfara, sa’annan sun lakada masa dan banzan duka, kuma suka daure shi tamau, daurin huhun goro a jikin wani falwaya. Allah ya sa mufi karfin zuciyanmu a ko da yaushe amin
Source :naij hausa
Title :
Wani Matashi Yayi Tsirara Yakuma Yi Filo Da Qur'ani A cikin Masallaci A Jihar Zamfara
Description : Kai jama’a, wai menene bukatar mutanen zamanin nan ne? Arziki, aure, yaya, ilimi, suna, ko me? Saboda a gaskiya yadda mutane ke kauce hanya ...
Rating :
5