Rigima ta cecekuce tsakanin wani mahaifi da dan sa kan kwallon Kashu a garin Obinetiti Isikwe Achi dake karamar hukumar Oji River ta jihar Enugu, ta yi sanadiyar salwantar rayuwar wannan matashi a ranar Larabar da ta gabata.
Rahotanni sun bayyana cewa, wannan mahaifi Hyacinth Ilo dan shekara 60 a duniya, ya rade kan dan sa, Izuchukwu Ilo, a yayin da cacar baki ta kaure a tsakanin su inda nan take ya fadi matacce.
Majiyar rahoton ta ruwaito cewa, mahaifin wannan matashi nan take ya haka rami kuma ya jefa gawar sa ciki bayan dokin zuciya ya yi sukuwa da shi da har ya kai ga wannan aika-aika.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, rigima ta mallakin kwallon Kashu ce ta janyo wannan abun takaici tsakanin Uba da dan sa.Kakakin rundunar 'yan sanda na jihar, Ebere Amaraizu, ya tabbatar da afkuwar wannan lamari da cewar tuni bincike ya kankama domin gurfanar da Mista Hyacinth a gaban Kuliya.
Jaridar naij com ta kuma ruwaito cewa, wata mahaifiya ta bayar da diyar ta jinginar bashin N100 da ya yi ma ta kanta a jihar Ebonyi.
Source :naij hausa
Title :
Wani Mahaifi Yakashe Dan Cikinsa A Enugu
Description : Rigima ta cecekuce tsakanin wani mahaifi da dan sa kan kwallon Kashu a garin Obinetiti Isikwe Achi dake karamar hukumar Oji River ta jihar E...
Rating :
5