Wani Jigo a Jam’iyyar adawa ta PDP kuma daya daga cikin manya a kasar Inyamurai Emmanuel Iwuanyawu ya bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi kokarin da ya dace ya nemi tazarce musamman idan aka duba lamarin Boko Haram.
Emmanuel Iwuanyawu yana ganin cewa Shugaban kasar yayi namijin kokari a shekaru kusan 3 da yayi yana mulki yace kuma irin su tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ko wani ba su isa su hana Shugaba Buhari neman takara a 2019 ba.
Iwuanyawu yace sai dai kar Shugaban kasar ya biyewa ‘yan kanzagin da ke kokarin zuga sa da ya dauki shawarar su da karfi da yaji. Shi dai Iwaunyawu yace bai yadda da dukkanin abin da Obasanjo ya fada a kan mulkin Buhari ba kwanaki a wasika.
Babban ‘Dan adawan yace har ‘yan shekaru 93 su na takara balle kuma irin su Shugaba Buhari da yake shekara 75. Sai dai Jigon na PDP yace akwai kuma wasu da ke neman tursasa Shugaban kasar har su na cewa za su kai shi Kotu inda bai yi takara ba.
Source :naij hausa
Title :
Wani Jigon Jam'iyyar PDP Ya Mara Buhari Baya Yazarce Har 2023
Description : Wani Jigo a Jam’iyyar adawa ta PDP kuma daya daga cikin manya a kasar Inyamurai Emmanuel Iwuanyawu ya bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu B...
Rating :
5