Wani dan Najeriya da ake kira Tresures Olawunmi Bayode ya kafa tarihi a duniya bayan ya kwashe kwanaki biyar ba kakkautawa yana karatu a bayyane.
Wannan shi ne karatu mafi tsawo da aka yi a cikin sa'oi 122 a kundin tarihi na duniya da ake kira Guinness World Record.
Yanzu haka dai Olawunmi shi ne aka nada 'Sarkin karatu na duniya.'
Rabon da a ga haka tun a shekara ta 2008, a yayin da Deepak Sharma Bajaan, dan kasar India, ya karanta littatafai 17 cikin sa'oi 113 da minti goma sha biyar.
Matashin ya shaidawa wakilin BBC Umar Shehu Elleman dalilin da ya zaburar da shi.
Ya ce "Wannan kokari ya faro ne a lokacin da mu ke tattaunawa da abokanai na game da muhinmancin neman ilimi idan abin a kwatanta ne da harkokin wasanni, shakatawa da kuma wakoki da kade-kade.
Ya ce wannan ne ya dalilin daya haifar da gardama tsakanin shi da abokansa. "Daga bangarensu sun yi imani cewa ta fannin wakoki da wasanni ne kadai ne za su iya kai wa zuwa wata kololuwa da kuma tara abin duniya ko samun kudi."
"To amma sai nace mu su ba haka lamarin yake ba, Na nuna mu su cewa ba a gina kasashen yammacin Turai bisa tsarin wasanni da wakoki da kade-kade ba, an gina yammacin Turai da ilimi ne"
"Gardama ta kaure a tsakaninmu da har ta kai saura kiris ya rage mu yi fada" a cewar Bayode.
Ana bincike kan yadda kafafen sada zumunta da wayoyi ke yi wa matasa illa
Ya ce wannan shi ne dalilin da ya zaburar da shi ya yi bajintar dogon karatu da zimmar nuna muhimmancin karatu ga masu tasowa.
Haka kuma yana fatan cusawa 'yan Afrika bukatar a sake lale domin farfado da karatu da neman ilimi a nahiyar.
Matashin ya ce shi kansa ya san ba karamin aiki ba ne ya daukar wa kansa domin mutum ya kwashe kwanaki biyar yana ta karatu ba ba abin wasa ba ne.
Dole Mutum ya hana idonsa barci da wasu bukatu da jiki ke marmari kamar hutu da dai sauransu. Ko da yake ya ce bayan duk sa'a daya yana samun hutu na minti biyar. Mr Bayode ya ce akwai wani lokaci da ya yi tunanin cewa mutuwa zai yi, domin zai ji kamar kamar yana cikin wata rayuwa da bai saba da irin ta ba.
Amma kuma duk da haka ya jajirce saboda nauyin da ya dorawa kansa, da kuma nunawa na gaba cewa ilimi jari ne. To ko ya Bayode ya ji da cewa a yanzu shi ne Sarkin karatu a duniya? Matashin ya ce ya yi wannan karatu ba wai domin ya nuna bajintar kafa wani tarihi da har za a ce wannan ne ya assasa ilimi.
"Abin da yake min dadi shi ne da kowa zai fadi cewa akwai wanda ya karanta tarin littatafai cikin kwanaki biyar wannan shi ne abin jin dadi na." "Buri na shi ne na tabbatar da cewa karatu ya sa mu bunkasa a nahiyar Africa" a cewar matashin.
Sannan ya ce ya yi haka ne domin ya cusawa masu tasowa da su kwana da sanin cewa ba wai wasanni da wakokoki ne za su kai su ga cimma burinsu ba, illa sai da ilimi domin shi ne makamin da za su rike. Wadanne irin Littatafai ne Bayode ya karanta? Bayode ya ce ya karanta manya da kananan littatafai.
Ya ce idan dalibai 'yan firamare suka shigo domin kallon kokarinsa, yakan dauko littatafan zube na Firamare ya karanta don ya karawa daliban kaimi.
Mr Bayode ya ce zai kai ziyara zuwa makarantu a Afirka, kuma zai fara da wasu jihohin Najeriya da suka hada da Legas zuwa Ogun da kuwa wasu kasashen Afirka da suka hada da Togo da Ivory Coast da Tanzania.
Kuma zai gudanar da ziyarar ne a kasashen domin yin kira a nemi ilimi, a yi karatu. "Mu na so mu fadawa duniya cewa duk wani abu na ilimi da aka dora bakar fata zai yi fice.
Cikin shekaru biyar masu zuwa za mu kasance a gaba ta fuskar ilimi da karatu a duniya", A cewar Bayode.
Source :bbc hausa
Title :
Wani Dan Nijeriya Ya Shafe Kwana Biyar Yana Zuba Karatu
Description : Wani dan Najeriya da ake kira Tresures Olawunmi Bayode ya kafa tarihi a duniya bayan ya kwashe kwanaki biyar ba kakkautawa yana karatu a bay...
Rating :
5