Daya daga cikin 'yan majalisar wakillai a Najeriya mai suna Honourable Julius Pondi ya yayata rabawa al'ummar da yake wakilta garin kwaki a matsayin kyauta a gare su.
Ganau dai sun shaidawa majiyar mu cewa garin kwakin da dan majalisar ya raba bai da wani yawan da har ya kai a yayata shi a kafar sadarwar zamani domin kuwa bai ma kai na Naira 200 ba a kasuwa.
A wani labarin kuma, Rahotannin da muke samu daga majiyoyin mu da dama na nuni ne da cewa jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party, PDP a takaice na cigaba da zawarcin Sanata Shehu Sani da ke wakiltar mazabar jihar Kaduna ta tsakiya ya dawo cikin ta.
Mun samu kuma dai cewa Sanatan na ta fuskantar matsin lamba daga bangarori da dama kuma mabanbanta da suka hada da kungiyoyin matasa da ma dattijai daga jam'iyyar ta PDP.
Source :naij hausa
Title :
Wani Dan Majalisan Tarayya Ya Raba Wa Jama’arsa Garin Kwaki
Description : Daya daga cikin 'yan majalisar wakillai a Najeriya mai suna Honourable Julius Pondi ya yayata rabawa al'ummar da yake wakilta garin ...
Rating :
5