Wata matashiya, Klariza Ruby Ochei, a dandalin sada zumunta na Facebook ta bayar da labarin yadda wani yaro ya kashe kansa ta hanyar shan gubar bera bayan faduwa jarrabawar JAMB a karo na hudu.
A wani rubutaccen sako da yaron ya bari kafin mutuwar sa, ya bayyana cewar ya dauki wannan mataki ne bayan mahaifiyar sa ta gargade shi da cewar muddin ya sake ya kara faduwa jarrabawar ta JAMB, to kada ya sake ya dawo masu gida.Ruby ta bayyana cewar, a takardar da yaron ya bari kafin ya sha gubar, ya koka a kan yadda mahaifiyar sa bata samun lokaci domin duba halin da yake ciki ko yadda al'amuran karatunsa ke tafiya.
A cewar Ruby, matashin ya rubuta jarrabawar a karo na farko kuma ya yi nasarar samun makin da ake bukata, saidai bai samu gurbi a jami'ar da ya nema ba. Ya sake rubutawa a shekarar da ta kara zagayowar amma ya kara fuskantar irin matsalar da ya samu a shekarar farko.Matashin, duk da haka, bai yanke kauna ba, saida ya sake rubuta jarrabawar amma sai ya gaza samun makin da ake bukata.
A wannan shekarar ne sai mahaifiyar sa ta yi korafin cewar ta gaji da asarar kudi a kansa duk shekara tare da gargadinsa cewar kada ya sake ya dawo gidansu muddin ya fadi jarrabawar. Hakan ya saka matashin shan guba bayan sakamakon na jarrabawar JAMB ya fito kuma bai yi nasara.
Source :naij hausa
Title :
Wani Dalibi Yasha Guba Bayan Faduwarsa Jarabawar Jamb
Description : Wata matashiya, Klariza Ruby Ochei, a dandalin sada zumunta na Facebook ta bayar da labarin yadda wani yaro ya kashe kansa ta hanyar shan gu...
Rating :
5