Aikin gama ya gama akan wani Almajiri da tsautsayi ya sanya ya rasa hannayen sa biyu a sanadiyar hukuncin malamin sa na makarantar Tsangaya a yankin Kagarawai dake wajen gari a jihar Gombe.
Wannan Almajiri mai shekaru 13 a duniya, Zubairu Yusha'u, ya gamu da bacin rana a sakamakon taka sahun barawo da yayi na daukar wata wayar salula a wani gida yayin da fita barar abinci da suka saba a ranar 3 ga watan Maris na 2018.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, bayan kwanaki uku da dauke wannan waya ta salula, sai kwatsam mai waya ta bayyana a makarantar Tsangaya mai dauke da dalibai sama 1500 kuma ta nemi cigiyar wayar ta da aka sace kamar yadda ta bayyana.
Wannan lamari ya sanya aka damko Zubairu kuma ya amsa da tabbas shine ya dauki wayar tare da bayar da hakuri da cewar yayi tunani ta gama amfani ne shi ya sanya aka jefar kuma ya dauko ta da har ta zamto abin wasa a gare shi.
Cikin fushi da daukar hukunci na shugaban wannan makaranta, Mallam Suraj Muhammad, ya lalubo igiya kuma ya daure hannayen Zubairu kuma ya kama gaban sa har na wasu tsawon lokuta.
A yayin da Zubairu ke yunkurin kubuta daga wannan mugun dauri da Malamin su ya yi masa, ya sanya hannayen sa suka kumbure da har ya gadar ma sa da rauni.
Mahaifin Zubairu Mallam Yusha'u ya bayyana cewa, ashe kwayoyin cuta sun shiga cikin wannan rauni na Zubairu da sai bayan kwanaki na bayar da magungunan gargajiya, an garzaya da shi asibiti kuma likitoci su ka tabbatar da cewa ba bu wata mafita face yanke hannayen biyu domin kar su harbi sauran sassan jikin sa.
A halin yanzu dai wannan lamari yana hannu jami'an tsaro na 'yan sanda, inda kwamishinan su Mr Tairu Shina Olukolu, ya bayar da umarnin binciken diddigi tare da damko wannan malami da ya shafe sama da shekaru 27 yana karantar da Almajirai.
Allah Ya Sauwake.... Amin
Source :naij hausa
Title :
Wani Almajiri Ya Rasa Hannayensa Guda Biyu A Gombe
Description : Aikin gama ya gama akan wani Almajiri da tsautsayi ya sanya ya rasa hannayen sa biyu a sanadiyar hukuncin malamin sa na makarantar Tsangaya ...
Rating :
5