Masu garkuwa da mutane kuma yan bindiga dadin ke ake damke kwanakin baya da suka bayyana cewa sanata Dino Melaye suke wa aiki sun arce daga kurkukun yan sanda.
A wannan karon, yan bindigan sun balle kurkukun jami’an yan sandan SARS da ke garin Lokoja, jihar Kogi tare da wasu da ke kurkukun can dama.Da aka tuntubi kwamishanan yan sandan jihar, Ali Jega, y ace ba zai iya cewa komai ba yanzu.
Zaku tuna cewa jaridar NAIJ ta kawo muku rahoton hukumar yan sandan Najeriya a ta damke yan daba 2 wadanda ke yiwa sanata mai wakiltan mazabar Kogi ta yamma a majalisan dattawa, Dino Melaye, domin kawo rikici lokacin zaben 2019.
Kakakin hukumar yan sandan, Jimoh Moshood, ya bayyana yan barandan masu suna Kabiru Saidu wanda akafi sani da Osama da Nuhu Salish, da jami’an SARS suka damke a jihar Kogi ranan 19 ga watan Junairu 2018 a Ogujeje, karamar hukumar Dekina na jihar Kogi.
Ya ce yan barandan sun bayyana da bakunansu cewa su mambobin wata kungiyar masu garkuwa da mutane ne kuma sunawa yan siyasa banga a jihar.
Source :naij hausa
Title :
Wadanda Ke Yiwa Dilo Melaye Aiki Sun Tsere Daga Hanun Yan Sanda
Description : Masu garkuwa da mutane kuma yan bindiga dadin ke ake damke kwanakin baya da suka bayyana cewa sanata Dino Melaye suke wa aiki sun arce daga ...
Rating :
5