Shugaban rundurar hukumar hana sha, da kuma fataucin miyagun kwayoyi ta kasa watau National Drug Law Enforcement Agency, NDLE a takaice na jihar Abia mai suna Mista Akindele Akingbade ya labarta yadda kwayar Tramadol tayi sanadiyyar mutuwar wani yaro dan Sakandare a jihar.
Yaron wanda ya fito daga karamar hukumar Ohafia ta jihar an ruwaito cewar ya mutu ne bayan ya sha kwaya 10 ta Tramadol din kamar dai yadda Mista Akindele Akingbade din ya bayyana yayin da yake gabatar da Lacca kan illolin shaye-shaye.
Jaridar naij ta samu cewa a wani labari kuma, Wasu gungun matasa 'yan jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress, APC da suka kira kansu masu ruwa da tsaki a jiya Alhamis sun bayyana karin wa'adin mulkin da aka yi wa shugaban jam'iyyar Cif John Odigie-Oyegun da mukarraban sa a matsayin abunda mai dace ba.
Matasan dai sun bayyana wannan matsayar ta su ne a yayin da suke wani taron manema labarai a garin Abuja jim kadan bayan kammala taron sirri da suka gudanar.
Source :naij hausa
Title :
Tramadol Ya Hallaka Wani Matashi A Abia
Description : Shugaban rundurar hukumar hana sha, da kuma fataucin miyagun kwayoyi ta kasa watau National Drug Law Enforcement Agency, NDLE a takaice na j...
Rating :
5