Hukumar kiyaye bautantar da mutane tana binciken lamarin fyade wanda ya hada da ma’aikacin kiyaye hadurra dake Makurdi, a jihar Binuwai, Charles Ali.
An Zargi Ali da laifin aikata fyade ga yarinya ‘yar primary mai shakaru tara. Yarinyar wadda mahaifinta makwabci ne ga Ali, a Kanshio, sun zargi cewa Ali yayi mata fyada a lokuta daban-daban har sau biyar.
Duk da cewa rahotanni da aka gabatar daga asibitin tarayya na jihar Makurdi, sun bayyan cewa tabbas an yiwa yarinyar fyade, amma dai ma’aikacin ya musanta cewa shine ya yi mata fyaden.
Ali ya dade yanayi mata fyaden tun shekarar 2017, har zuwa watan Fabrairu 26, lokacin da aka kamashi yana mata fyaden a cikin motarsa da ya ajiye can nesa da gidanda suke zama. Inda jaridar Punch, ta bayar da rahoton cewa wata mai talla ce mai suna Chinasa, ta ganshi yanawa yarinyar fyade a cikin motar.
An samu labarinn cewa Ali ya nemi gafara daga mahaifin yarinyar lokacin da labarn fyaden ya bazu a cikin unguwa, amma ya musanta maganganun nasa lokacin da aka kai rahoto ga hukumar NAPTIP.
Source :naij hausa
Title :
Tir:Wani Ma'aikacin FRSC Yayi Ma Wata Yar Firarmare Fyade Har Sau Biyar
Description : Hukumar kiyaye bautantar da mutane tana binciken lamarin fyade wanda ya hada da ma’aikacin kiyaye hadurra dake Makurdi, a jihar Binuwai, Cha...
Rating :
5