Wani direban mota dan shekara 42, Seyi Oluwukere, ya shiga hannun hukumar 'yan sanda a jihar Legas da laifin lalata da wani karamin yaro inda ya kuma ce ya aikata hakan wasu mutane bakwai daban da suka hadar har da manya.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, wannan malalaci dai ya yaudari karamin yaron ne tun daga filin su na buga kwallo har zuwa dakin sa dake kan hanyar Marshal ta unguwar Surulere a jihar Legas inda ya aikata wannan alfasha.
A cewar wannan karamin yaro dan shekara 12 da ba a bayyana sunan sa ba, "Mista Seyi dai ya janye shi daga filin wasa tare har zuwa dakin sa a bisa yaudara ta alkawarin taimakon sa da zai yi a harkar waka kasancewar sa mawaki.
""Zuwan su dakin ke da wuya, Seyi ya kwale kayan sa kuma ya umarci yaron da ya aikata kuma ya yi ba tare da wata kyuya ba, inda ya zakke ma sa ta dubura.
"Wannan lamari ya sanya yaron ya gaza samun sukuni da har ya sanya ya labartawa iyayen sa halin da ya ciki inda su ka danganta lamarin ga hukumar 'yan sanda.
Source :naij hausa
Title :
Tir:Nayi Lalata Da Kananun Yara Da Manya 8 - Wani Direba
Description : Wani direban mota dan shekara 42, Seyi Oluwukere, ya shiga hannun hukumar 'yan sanda a jihar Legas da laifin lalata da wani karamin yaro...
Rating :
5