Akalla kananan yara guda ashirin ne suka rigamu gidan gaskiya a jihar Jigawa a sakamakon yaduwar cutar sankarau a jihar, kamar yadda rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar. Mace macen kananan yaran a sanadiyyar cutar ya fi muni a kauyen Majia, dake cikin karamar hukumar Taura, inda aka ruwaito kananan yara guda tare ne suka mutu, inji rahoton majiyar Jaridar Naij.
Rahotanni sun tabbatar da mutuwar sama da yara 20, a sakamakon yaduwar cutar sankarau zuwa sauran kananan hukumomin jihar, kuma yawancinsu basu wuce shekara 3-13 ba. Allurar sankarau Wani uban da ya rasa yarsa Hadiza mai shekaru 3, Malam Ali Sunusi, ya bayyana cewa yarsa Hadiza ta gamu da ajalinta ne a sanadiyyar cutar sankarau, inda yace alamomin cutar na farawa ne da ciwon kai mai tsanani, amai da zawo.
Da aka tuntubi kwamishinan kula da kiwon lafiya na jihar, Abba Zakari, shima ya tabbatar da yaduwarsa cutarm sa’annan ya yi alkawarin daukan matakan shawo kanta. Ita dai cutar na farawa ne a lokacin da tantanin dake kare kwakwlawa ya kumbura.
Source :naij hausa
Title :
Ta'adin Da Cutar SanKarau Yayi A Jihar Jigawa
Description : Akalla kananan yara guda ashirin ne suka rigamu gidan gaskiya a jihar Jigawa a sakamakon yaduwar cutar sankarau a jihar, kamar yadda rahoton...
Rating :
5