A yayin biki na bude gasar Al-Qur'ani ta kasa karo na 32 da aka gudanar a jihar Katsina, Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubukar III, ya soki wasu malaman addini da suka dauki salon shiga ta kwalisa yayin bayyana gaban al'umma.
Sarkin ya bayyana damuwar sa dangane da yadda malaman ke holewa ta hanyar shiga tsala-tsalan motoci da kuma kwanciya a gidaddaji na alfarma.
Mai martaba sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumin Kabir Usman, shine ya wakilci Sultan a yayin gasar ta Al-Qur'ani, inda ya bayyana takaicin sa dangane da yadda malamai ke kwalisa a madadin su zamto madubin dubawa ga al'umma.
A yayin da wannan batu zai bakantawa 'yan kwalisar Malamai, sai dai ko shakka babu gaskiya guda ce kuma daga kin ta sai bata kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, inda ta bayar da misalan magabatan malamai masu tawali'u da kankan da kai.
Source :naij hausa
Title :
Sultan Din Sokkoto Ya Caccaki Wasu Malaman Addini
Description : A yayin biki na bude gasar Al-Qur'ani ta kasa karo na 32 da aka gudanar a jihar Katsina, Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubuk...
Rating :
5