An haifi Malam Malam Muhammadu Aminu Sambo ne a shekarar 1888 a garinn Zazzau, kuma ya rasu ne a 1961. Yana daga cikin samarin farko da Boko ta taras a Zaria, inda ya zama mai jin turanci, kuma dan boko da har sai da ya jagoranci Turawan mulkin mallaka shawagin kidaya.
A shekarar 1923 ya zama dan boko na farko a birnin Zazzau da ya fidda Sarki Kwasau da ma mutan Zariya daga kunya, inda har Sarki Ibrahim dan Kwasau ya nada shi Jagora ga tawagar Birtaniya da Sarki George ya aiko don yin nazarin dukan kabilan arewacin Najeriya lokacin mulkin mallaka.
A zamanin nan da jama'ar Arewa ke ganin kamar ilimin Boko bashi da wani alfanu, su irin wadannan dattijai sunyi wa kansu kiyamul-laili, inda suka rungumi zamani, kuma zamanin ya karbe su ya tafi tare da su, ba tare da sun yada al'adarsu ba.
Source :naij hausa
Title :
Shin Kunsan Waye Dan Boko Na Farko A Garin Zazzau?
Description : An haifi Malam Malam Muhammadu Aminu Sambo ne a shekarar 1888 a garinn Zazzau, kuma ya rasu ne a 1961. Yana daga cikin samarin farko da Boko...
Rating :
5