Bincike daga fadar shugaban kasa ta tabbatar da samuwar wani karamin yaro a cikin yan matan Dapchi guda 104 da kungiyar ta’addanci ta sako a ranar Laraba 21 ga watan Maris.
Rahotannin da jaridar naij ta samu daga fadar shugaban kasar ta tabbatar da cewa sunan wannan karamin yaro Mala, kuma yana da ne ga wani Malami dake koyarwa a kwalejin yan matan dake garin Dapchi.
Majiyar NAIJ ta ruwaito har da wannan yaro mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram suka tattara tare da yan mata 110 suka yi awon gaba da su a ranar 19 ga watan Feburairu.
Idan za’a tuna, yan ta’addan sun far ma sakandarin kimiyya na yan mata ne dake garin Dapchi da misalin karfe 10 na safiyyar ranar 19 ga watan Feburairu a lokacin da daliban ke hutun tara, inda suka dinga harbe harbe a sama, har sai da suka kammala dauke yan matan.
Sai dai kimanin wata guda a da sace yan matan, kuma sakamakon wata tattaunawa da gwamnati ta shiga da kungiyar, an samu nasarar shawo kan kungiyar, inda ta yarda ta dawo dasu da kanta har garin Dapchi, ba tare da bukatar kudi ko musayar fursuna ba, kamar yadda gwamnati ta tabbatar.
Source :naij hausa
Title :
Shin Kunsan Wanene Yaron Da Aka Sake Tare Da Yan Matan Dapchi?
Description : Bincike daga fadar shugaban kasa ta tabbatar da samuwar wani karamin yaro a cikin yan matan Dapchi guda 104 da kungiyar ta’addanci ta sako a...
Rating :
5