Gwamnatin tarayya tace, yanzu haka tana kara yawan manoman shinkafa a kasar, a kokarin da takeyi na mayar da Najeriya mai dogaro da kanta bangaren samar da shinkafa.Jaridar Punch ta ruwaito cewa, Lai Mohammed, wanda shine Ministan labarai ya bayyana haka lokacin daya kai ziyara a wasu gonakin shinkafa.
Yace kuma ce yana da muhummanci ga Najeriya ta jawo hankalin mutane zuwa ga kasuwancin shinkafa, inda ya bayyana cewa manoman shinkafar sun karu daga miliyan biyar zuwa miliyan 12 cikin shekaru biyu.Ministan yace, “Mun kara yawan manoman shinkafa daga miliyan biyar zuwa miliyan sha biyu a yanzu.
Kuma yanzu haka akwai harkar aikin noman da za’ayi bana wanda za’a noma shinkafa a gona mai fadin hekta 200,000. Kuma kowace hekta za’a dauki mutane 25; yanda zamu samu wasu mutane miliyan biyar da zasu karu a cikin manoman shinkafa.
A kalla manoma 31,000 ne suka samu tallafi daga bankin Najeriya a karkashin jihar Kano wannan shakarar inda suke noma fili misalin hecta 200,000 a halin yanzu.
”Mohammed yace, akwai wasu jihohi 21 da suka nuna sha’awa kan harkar tare da jihar Kebbi wadda dama itace wadda akafi sani da harkar.Bayan haka, Gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, yace, cikin shekaru biyu, noman shinkafa ya karu daga tan 5.7m zuwa tan 17m, a shekara, a rahoton Leadership.
Jaridar naij ta ruwaito cewa, ya bayyana hakan ne ga mai bayar da rahoto na fadar shugaban kasa bayan sun gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari, a fadarsa. Gwamnan yace, an bude kamfanoni takwas na shinkafa a shekarar data gabata, wanda ya kara yawan samar da shinkafa.
Source :naij hausa
Title :
Shigo Da Shinkafa Kasarnan Ya Ragu Har Kashi 90% - Lai Muhammad
Description : Gwamnatin tarayya tace, yanzu haka tana kara yawan manoman shinkafa a kasar, a kokarin da takeyi na mayar da Najeriya mai dogaro da kanta ba...
Rating :
5