Kwamared Shehu Sani wanda shi ne Sanatan Kaduna ta tsakiya ya caccaki Gwamnatin Tarayya da kuma masu sukar mai kudin Duniya watau Bill Gates kan wasu kalaman da yayi kwanan nan.
A makon da ya gabata ne Bill Gates yace akwai matsala a tsarin tattalin arzikin Shugaban kasa Buhari. Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo dai da irin su Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ba su yi na’am da wannan ba.
Shehu Sani yayi amfani da shafin san a Tuwita yace ida Bill Gates ya kawo gudumuwar makudan kudi a Najeriya sai a karbe ana rawar jiki. Amma kuma idan ya bada shawara, sai a koma ana sukar sa ana cewa yana zagin Gwamatin kasa.
Fitaccen Sanatan na Jihar Kaduna dai yana ganin duk wanda ya duka kasa ya karbi tallafin kudin Bill Gates, to ya kuwa kamata ya karbi shawarar sa kamar yadda ya karbi Miliyoyin Dalolin sa.
Source :naij hausa
Title :
Shehu Sani Ya Caccaki Gwamnatin APC Da Fadar Shugaban Kasa
Description : Kwamared Shehu Sani wanda shi ne Sanatan Kaduna ta tsakiya ya caccaki Gwamnatin Tarayya da kuma masu sukar mai kudin Duniya watau Bill Gates...
Rating :
5