Masauratar kasar Saudiya ta dauki nauyin gina masallatai 200 a kasar Jamus, a sakamakon adadin 'yan gudun hijra na kasar Syria dake ta hauhawa wajen neman mafaka a kasar.
Ana ci gaba da suka tare da kalubalantar wasu kasashen larabawa masu arziki dake makwabtaka da kasar Syria, sakamakon rashin tallafa mata dangane da matsalolin jin kai da take fama da shi.
Wadannan kasashe da duniya ke kalubalanta sun hadar da; Qatar, Oman, UAE, Bahrain, Kuwait da kuma Saudiyya.
Da sanadin wata jaridar kasar Lebanon mai sunan Al Diyar mun samu rahoton cewa, Saudiya na kokarin wanke wannan kashi da ake goga mata, inda za ta gina masallatai 200 da kowane daya zai dauki 'yan gudun hijira 100 na Syria a kasar ta Jamus.
Wasu adalan rahotanni sun bayyana cewa, kasashen da duniya ke kalubalanta sun yi tarayya wajen bayar da mafaka ga miliyoyan 'yan gudun hijra na Syria a yayin da rikicin ya huro kai tun a shekarar 2011.
Source :naij hausa
Title :
Saudiyya Zata Gina Masallatai 200 A Jamus
Description : Masauratar kasar Saudiya ta dauki nauyin gina masallatai 200 a kasar Jamus, a sakamakon adadin 'yan gudun hijra na kasar Syria dake ta h...
Rating :
5