Wani dan saurayi ya ga samu ya ga rashi a kasar Indiya, inda ana saura kwana guda a daura masa aure da sahibarsa, abin kaunarsa, kwatsam sai ta ce ta fasa, ai ba dole bane, kuma bata yi, sai dai dalilinta akwai ban mamaki.
The Punch ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a kauyen Sugauli, dake yankin Bihar na kasar Indiya, inda matashin mai suna Dakta Ravi Kumar, ma’aikacin likita ya kwashe shekara guda yana shirye shiryen aurensa, kuma komai ya tafi dai dai.
An sha bukukuwan kafin aure da dama duk a shirin zuwan ranar daurin auren, har sai da aka ka saura kwana guda a daura auren, inda a yayin da ake gudanar da wasu al’adunsu na kasar Indiya dake bukatar ango ya cire hularsa, cire hular tasa ke da wuya sai Amaryar ta hangi sanko a kansa, daga na tace fau fau fau! Ba ta yi, a kai kasuwa.
Abinka da bukatar dan Adam, duk kokarin da yan uwa da abokan arziki suka yi na ganin sun shawo kan wannan amaryar gobe ya ci tura, aka kada aka kai mari, ita kuwa tace ai sai ku yi, na fasa, babu yadda za’yi na auri mai sanko, haka kuwa aka yi, dole aka kashe maganan auren.
To amma da yake Allah mai sakayya ne, kuma shi ma matashin ya dage sai ya koma gida da mata, nan da nan suka kutsa kai da yan uwansa cikin kauyen tsohuwar budurwar tasa, inda suka ci karo da wata tsaleliyar budurwa mai suna Neha Kumari, ta ce ta ji ta gani, Allah ya kashe ya bata, nan da nan aka daura musu aure.
Source :naij hausa
Title :
Sanko Ya Hana Wata Budurwa Auren Samarinta
Description : Wani dan saurayi ya ga samu ya ga rashi a kasar Indiya, inda ana saura kwana guda a daura masa aure da sahibarsa, abin kaunarsa, kwatsam sai...
Rating :
5