Tsohon shugaban kasa Obasanjo, a yau Alhamis, ya bayyana cewar sabuwar kungiyar sa (CMN) da ya kafa domin kwace mulki daga hannun jam'iyyar APC a 2019, na da magoya bayan ma su rijista da adadinsu ya kai miliyan uku.
Ya yi kira ga 'yan Najeriya da su malllaka tare da adana katin zabensu na dun-dun-dun.
Obasanjo na wadannan kalamai ne yayin wani taro a kan matan Najeriya da aka gudanar a Otal din Eko dake garin Legas. Ya ce kungiyar sa zata hada kai da ragowar kungiyoyin gwagwarmaya domin fitar da Najeriya daga halin da take ciki.
Ya kara da cewar zai dauki nauyin mutane daga mambobin kungiyar sa domin yin takara bayan CMN ta rikide ya zuwa jam'iyyar siyasa.Tsohon shugaban kasar ya jajantawa matan tare da nuna bakincikinsa cewar har yanzu babu wata mace a Najeriya da ta taba zama gwamna ko shugabar majalisa ko wani babban mukami a kasar nan.
Obasanjo ya karfafa wa mata gwuiwar fitowa a dama da su a siyasar Najeriya."Ku daina yarda wasu na tsara ma ku rayuwa. Ku tsara rayuwar ku da kan ku. Tabbas, mata na bukatar a karfafa ma su gwuiwa amma ya zama tilas su fara taimakon kansu tukunna," a cewar Obasanjo.
Tsohon shugaban kasa Obasanjo, ya yi shura wajen sukar shugabannin Najeriya dake kan mulki, don a kwanakin baya saida ya shawarci shugaba Buhari da kul ya kuskura ya sake fitowa takarar shugabancin kasa a zaben shekarar 2019.
Source :naij hausa
Title :
Sakon Obasanjo Ga Dukkan Matan Nijeriya
Description : Tsohon shugaban kasa Obasanjo, a yau Alhamis, ya bayyana cewar sabuwar kungiyar sa (CMN) da ya kafa domin kwace mulki daga hannun jam'iy...
Rating :
5