A kwanan nan mu ka ji cewa Sakataren yada labarai na Jam’iyyar APC a Jihar Zamfara Sani Gwamna Mayanchi yace ba su amince da karin wa’adin da aka yi wa Shugabannin Jam’iyyar APC ba.
Sani Mayanchi yace su na kalubalantar kujerar Shugaban APC na kasa watau Cif John Odigie-Oyegun da sauran mukarraban sa ne a Kotu domin wa’adin da aka kara masu ya sabawa dokar Najeriay da ka’idar su ta Jam’iyyar APC mai mulki.
Sakataren yada labaran Jam’iyyar yace sun garzaya babban kotun Tarayya da ke Abuja domin ganin an dakatar da wa’adin da aka karawa Shugabannin Jam’iyyar. Mayanchi yace abin da ya kamata shi ne ayi sabon zabe domin fitar da Shugabanni.Yanzu dai an sa ranar shari’a nan da kwanaki 5 a Kotu a Abuja.
‘Ya ‘yan APC da su ka kai kara sun kafa hujja da sashe na 223 na tsarin mulki da bangare na 13 da 17 na dokar Jam’iyyar APC da tace ta zabe ake fitar da masu jan ragamar Jam'iyya.
Source :naij hausa
Title :
Sabon Rikici Ya Tashi A Jam'iyyar APC
Description : A kwanan nan mu ka ji cewa Sakataren yada labarai na Jam’iyyar APC a Jihar Zamfara Sani Gwamna Mayanchi yace ba su amince da karin wa’adin d...
Rating :
5