Babban ‘Dan jaridan nan kuma mai gidan Jaridar Sahara Reporters Yele Sowore ya dage cewa zai fito takarar Shugaban kasar Najeriya a zabe mai zuwa inda yace zai ba Shugaba Muhammadu Buhari kashi.
Tun a watan Jiya Yele Sowore ya bayyana cewa za a gwabza da shi a zabe mai zuwa. Yanzu dai ta tabbata cewa ‘Dan jaridar ba da wasa ya ke yi ba inda har ya fara shirin neman kudin yakin neman zabe domin hawa karagar mulki.
Sowore yace idan ya karbi mulkin Najeriya za a zuba ayyuka na more rayuwa. Bayan nan kuma yayi alkawarin kara albashin Ma’aikata zuwa N100, 000. ‘Dan jaridar da ke Amurka yace Shugaba Buhari ba zai iya samawa matasa aiki ba.
Kafin nan dai Sowore yayi shugabancin matasa lokacin yana ‘Dan makaranta don haka yace ba yau ya fara jagoranci ba. A jawabin na sa yayi kaca-kaca da manyan kasar irin su Bola Tinubu, Gwamna Ambode, Aliko Dangote da sauran su.
Source :naij hausa
Title :
Sabon Abokin Hamayyar Muhammadu Buhari
Description : Babban ‘Dan jaridan nan kuma mai gidan Jaridar Sahara Reporters Yele Sowore ya dage cewa zai fito takarar Shugaban kasar Najeriya a zabe mai...
Rating :
5