Mun samu labari daga Jaridar Vanguard a farkon makon nan cewa Tsagerun Yankin Neja-Delta sun sha alwashin za su koma barnar da su ka saba idan Shugaban kasa Muhammadu Buhari bai biya masu wata bukatar su ba.
Kungiyoyi kusan 10 har da wani bangare na Niger Delta Avengers sun ba Shugaba Muhammadu Buhari wata guda ya dawo da tsohon Shugaban tsarin da ake ba 'Yan Neja-Delta lamuni watau Birgediya Janar Paul Boroh (mai ritaya) bakin aiki.
Tsagerun na Yankin Neja-Delta sun nemi Shugaban kasa Buhari ya sake shawara na korar Janar Boroh da yayi daga aiki. Idan ba haka ba Tsagerun za su koma fasa bututun man kasar domin kowa ya dandana kudar sa Inji wani Jagoran su.
Johnmark Ezonbi yace za su fasa duk wani bututun mai da ake ji da shi na kasar idan har ba'a dawo da Paul Boroh aiki ba. Ezonbi yace Boroh ne yayi kutun-kutun wajen ganin sun daina barnar da su ke yi aka yi sulhu da Gwamnatin Tarayya.
Source :naij hausa
Title :
Sabbin Sharudan Yan Naija Delta Zuwa Ga Shugaba Buhari
Description : Mun samu labari daga Jaridar Vanguard a farkon makon nan cewa Tsagerun Yankin Neja-Delta sun sha alwashin za su koma barnar da su ka saba id...
Rating :
5