Sanannar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood da ma kuma turanci a masana'antar Nollywood watau Rahama Sadau ta bayyana rungume-rungumen da suka yi a cikin wakar da ta yi da mawakin nan Classiq a shekararun baya a matsayin tsautsayi da kuma kaddara.
Jarumar ta bayyana hakan ne a cikin wata fira da ta gabatar da wakilin majiyar mu ta Mujallar Fim a cikin wani yanayi mai cike da nadama da kuma ban tausayi.
Da aka tambaye ta ko daman ta taba yi wa kungiyar masu shirya fina-finan Hausa ta MOPPAN da suka dakatar da ita, sai jarumar ta ce a'a.
Yanzu haka dai jarumar kamar yadda muka samu na a cikin wani hali na rashin tabbas da kuma sanin sahihiyar matsayar ta a masana'antar ta Kannywood bayan da kungiyar ta MOPPAN ta shigar da kara a kotu biyo bayan yafe mata da gwamnatin jihar Kano da kuma masarautar jihar ta Kano suka yi.
Source :naij hausa
Title :
Runguma Juna Da Mukayi Da Classiq Tsautsayi ne-Rahma Sadau
Description : Sanannar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood da ma kuma turanci a masana'antar Nollywood watau Rahama Sadau ta ...
Rating :
5