Gwannan Jihar Kogi Alhaji Dino Melaye yayi kaca-kaca da Sanatan Jiharsa ta Yamma watau Dino Melaye bayan yayi wani bidiyo inda ya gargade sa a kwanan nan. Bello yace surutun banza Sanatan yake yi.
Gwamna Yahaya Bello ya bayyanawa 'Yan Jarida a gidan Gwamnati cewa ba abu bane mai sauki mulkar Jihar Kogi inda yace yana bakin kokarin sa a matsayin sa na Gwamnawajen yin aikin gaban sa kuma mutane su na yabawa kokarin na sa.
Yahaya Bello yake cewa surutun banza na wani can dabam ba zai hana shi aikin sa ba. Gwamnan ya tabbatar da cewa yayi takaicin kashe-kashen da ya faru kwanaki a wani Yankin Jihar inda yace ya garzaya wurin kuma ya dauki mataki.
Daily Trust ta rahoto Mai girma Gwamnan Alhaji Yahaya Bello yace an taba samun lokacin da aka rasa rayuka da dama a 2014 kafin ya zama Gwamnan Jihar. Bayan nan Jami'an tsaro sun yi bakin kokarin su na kawo zaman lafiya a Yankin Jihar.
Source :naij hausa
Title :
Rikici Ya Barke Tsakanin Dilo Melaye Da Gwamnan Kogi
Description : Gwannan Jihar Kogi Alhaji Dino Melaye yayi kaca-kaca da Sanatan Jiharsa ta Yamma watau Dino Melaye bayan yayi wani bidiyo inda ya gargade sa...
Rating :
5